1 Corinthians 12

Baye-bayen Ruhaniya

1To, game da baye-baye na ruhaniya, ʼyanʼuwa, ba na so ku kasance da rashin sani. 2Kun san cewa saʼad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana. 3Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu laʼananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.

4Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. 5Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji ɗaya ne. 6Akwai aiki iri iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.

7An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.

12Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi. 13Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda-ko Yahudawa ko Helenawa, bawa ko ʼyantacce-an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha.

14To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa. 15Da ƙafa za ta ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba. 16Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba. 17Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma dukan jiki kunne ne, da me za a sunsuna? 18Hakika, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama. 19Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.

21Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!” 22A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci. 23Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Saʼan nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu, 24gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani, 25don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna. 26In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.

27To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, saʼan nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, saʼan nan kuma masu magana da harsuna iri iri. 29Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? 30Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? 31Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma.

Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.

Copyright information for HauSRK